Fast & Easy Contact??
08025077766 || BBM: D602DF00
Promote or Advertise & Placement Product
Info@9jabasic.Net
FacebookTwitterInstagram


« | »

Intro
Uhn uhn uhn
Bmeri , Abooooki , Takson
Landmark on the beat.

Verse 1
Bare mukaje daurin auren kyakyawa fauzihyah
Sauran kadan bana da my koma taaziyah
Kyau ango afuskane sai mugun hali
Baisan komaiba sai wulakanta iyali
Duka, zagi, habaici, kiyaya
Taki gayawa manya gata mai biyaya
Meyasa muka fadawa kogin so bamagani
Meyasa muke fadawa son maison wani

Chorus
Akwai wata yarinya sunanta fauziyah
Ga kyau, ga kuma hima, ga illimi wajen fauziyah
Ama rashin dacenta, da mujin da ya aureta
Baisan bai cancanta ya Auri kamar fauziyah
Kullun saiya zageta
Kullun saiya mareta
Kullun saiya duketaaaa
Wayo Allah,

karabamu da ciwon so ( Ciwon So )
Karabamu da ciwon so ( Ciwon So )
Karabamu da ciwon soyayyaaa, wayo Allah…X2

Tabasa zuciyata amma yaci amana
Hargi tsatse bayakomai cikin lumana
Afuska kamar danmutun a zuciyashi Dodo
Cefanema ya daina baisiyan ko soso
Ko tamutu ko tayi rai shiko oho
Gabakar magana kamar bakinsa na yoyo
Wai tanason mijinta toh saiya kasheki
Duba fatan jikinki haryanzu tana sheki
Duba madubi kigani anya wanan kece
Kin riga kin kama ganye kin saki reshe
Kinada zufin ciki saikace rijiya
Kece amaryasa kuma kece kishiya
Har fada yakeyi wai matasa bazuciya
Daya shigo zatace mekakeso nayima
Wanan butulci nasa da mai yayi kama
Yakamata muyi wani abu haba jamaa

Kuliyaumin cikin jinya
Batafita Dan kunya
Fuskanta maishaawa
Takoma kamar tukunya
Yakamata mu hanzarta
Yakamata mu gagauta
Yakamata mu kokarta
Muceci ran fauziyah

Kullum saiya cuceta
Kullun saiya nausheta
Kullun saiya koretaaa
Wayo Allah

karabamu da ciwon so ( ciwon so)
Karabamu da ciwon so ( Ciwon soo)
Karabamu da ciwon soyayyaaa, wayo Allah…X2

Wayo Fauziyah
Wayo Fauziyaah
Wayo Fauziyaaah

Tags:

Categories: Lyrics

About Author

About

Is A Young Geek By Passion & A Blogger By Profession, A Part Time Blogger Living In Nigeria, The Founder & CEO Of 9jabasic.Net Media.

« | »